Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Inter Milan na shirin kawo karshen kwantiragin Eriksen na Denmark

Kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan ta sanar da shirin kawo karshen kwantiragin Christian Eriksen na Denmark bayan matsalar zuciyar da dan wasan ya samu wanda masana suka ce zai yi wuya ya iya ci gaba da taka leda a rayuwarsa.

Karramawar da aka yiwa Christian Eriksen.
Karramawar da aka yiwa Christian Eriksen. HANNAH MCKAY POOL/AFP
Talla

Eriksen mai shekaru 29 na da sauran kwantiragi da Inter Milan amma kuma sanarwar da kungiyar ta fitar ta ce ta na duba yiwuwar kawo karshen kwantiragin dan wasan wanda rabonsa da taka leda tun bayan faduwarsa a watan Yunin da ya gabata lokacin da ake tsaka da gasar EURO sakamakon bugawar zuciya.

Duk da cewa dan wasan ya fara atisaye a gida bayan fara murmurewa amma kungiyar ta serie A na ganin abu ne mai wuya Eriksen ya iya komawa taka leda kamar yadda ya ke a baya, duk da bukatar hakan da ya nuna.

Acewar kungiyar yanzu haka tana tsaka da tattaunawa ne kan yadda za su rabu da Eriksen.

A karshen kakar wasa ta bara ne Eriksen ya koma Inter Milan daga Tottenham ta Ingila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.