Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Eriksen na Inter Milan ya koma atisaye karon farko bayan bugun zuciya

Dan wasan tsakiya na Denmark Christian Eriksen ya koma atisaye yau alhamis karon farko bayan faduwarsa sakamakon bugun zuciya lokacin da ake tsaka da wasannin gasar EURO.

Tun cikin watan Yunin da ya gabata, Christian Eriksen ya gamu da matsalar bugawar zuciya.
Tun cikin watan Yunin da ya gabata, Christian Eriksen ya gamu da matsalar bugawar zuciya. Reuters/Andrew Couldridge
Talla

Cikin watan Yunin da ya gabata ne lokacin da ake tsaka da wasa Eriksen ya fadi inda lumfashinsa ya dauke matakin da ya kai ga dakatar da wasansu na wancan lokaci don bashi taimakon gaggawa kafin daga bisani bincike ya gano cewa ya samu bugawar zuciya ne.

Jaridun wasanni na Denmark sun ruwaito cewa Eriksen mai shekaru 29 ya gudanar da atisayen nasa na yau ne  da kungiyarsa ta yarinta wato Odense da ke cikin kasar.  

Duk da cewa dan wasan na Denmark na da sauran kwantiragi da Inter Milan amma dashen da akayi masa a zuciya bayan samun matsalar ta bugawar zuciya bazai samu sukunin iya ci gaba da taka leda karkashin gasar Serie A ba.

Akwai dai masana da ke ganin abu ne mai wuya Eriksen ya iya sake taka leda a rayuwarsa.

Sai dai manajan Odense Michael Hemmingsen da ke tabbatar da atisayen Eriksen tare da tawagar ta shi a Adalen ya ce dan wasan na da cikakkiyar lafiyar iya taka leda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.