Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Eriksen ya sa hotonsa a Instagram karon farko bayan faduwa a filin wasa

Dan wasan tsakiya na Denmark Christian Eriksen ya wallafa hotonsa yau talata a shafinsa na Instagram daga gadon asibitin da ya ke kwance hoton da ke matsayin irinsa na farko da dan wasan ya fitar tun bayan faduwarsa a karawarsu da Finland ranar Asabar din da ta gabata.

Dan wasan tsakiya na Denmark Christian Eriksen a wani sako da ya saki ta shafinsa na Instagram yau talata.
Dan wasan tsakiya na Denmark Christian Eriksen a wani sako da ya saki ta shafinsa na Instagram yau talata. © chriseriksen8
Talla

Eriksen mai shekaru 29 da ke taka leda a Inter Milan a minti na 43 da fara wasan na ranar asabar ne ya yanke jiki ya fadi bayan bugawar zuciya da kuma toshewar hanyoyin lumfashi wanda ya tilasta dakatar da wasan gabanin komawa.

A kasan hoton na Eriksen da ke kwance a gadon asibiti, ya rubuta cewa ya fara samun sauki ko da ya ke akwai sauran gwaje-gwaje da zai yi gabanin murmurewa.

Sakon na Eriksen ya ci gaba da jinjinawa miliyoyin al’ummar Duniya da suka jimama faduwar tasa, wanda ya ce shi da iyalinsa na alfahari da hakan, sakon da tuni mutane fiye da miliyan hudu suka gani tare da yin martani.

Eriksen wanda ya shafe akalla mintuna 15 ba tare da motsi ba a filin wasan duk da taimakon tawagar bayar da agaji, gabanin gaggauta kai shi asibiti,  akwai likitocin da ke bayyana shakku kan yiwuwar ya iya sake taka leda a rayuwarsa, ko da ya ke har yanzu hukumar kwallon kafar Denmark da tawagar likitocinta basu ce uffan ba game da makomar dan wasan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.