Rasha na daukar matakan kare mahalarta EURO 2020 daga korona
Mahukunta a Saint Petersburg, wadanda ke shirin karban bakwancin wasu jerin wasannin gasar Euro 2020, sun bayyana matakin kara tsaurara matakan hana yaduwar cutar corona a kokarinsu na dakile bazuwar cutar.
Wallafawa ranar:
Jami’ai a Saint Petersburg, birni na biyu da cutar tafi yiwa illa a kasar Rasha baya ga Moscow da ake sa ran za ta karbi dubban magoya bayan kwallan kafa daga Turai, sun bayyana daukar dukkan matakan da suka dace don kare magoya baya da ‘yan wasa a lokacin wasannin na kwallon kafa mafi girma a nahiyar Turai.
Matakan da za'a dauka
Cikin matakan da aka dauka, daga ranar Alhamis gidajen abinci da wuraren wasan yara a manyan kantuna zasu kasance a rufe, sannan za’a hana sayar da abinci a bangaren ‘yan kallo da magoya baya.
Kazalika gidajen Cinema zasu rage ‘yan kallo zuwa kashi 50 cikin ɗari, ƙasa da kashi 75 da suke dauka yanzu haka, kuma za a rufe gidajen abinci tsakanin karfe biyu na safe da kuma 6 na safe.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu