Gasar Euro 2020: Rana ba ta karya
A wannan Juma’ar ake fara gasar cin kofin kasashen Turai da ake kira Euro 2020 wanda annobar korona ta hana gudanar da shi bara.
Wallafawa ranar:
Gasar wadda tsohon shugaban hukumar kwallon kafar Turai Michel Platini ya bayyana za’a dinga zagayawa da ita tsakanin kasashen dake yankin a wannan karo za’a gudanar da ita ne a gaban takaitattun yan kallo saboda dokokin kula da lafiya.
A wasan farko na gasar za’a kara ne tsakanin kasar Italia da Turkiya a filin wasan Stadio Olimpico dake birnin Rome.
Kasar Faransa ke sahun gaba cikin jerin kasashen da ake saran su lashe gasar saboda fitattun Yan wasan da take da su da yanzu haka suke tashe a duniya.
Jaridar L’Equipe ta kasar a sharhin da tayi kan gasar ta wallafa hotunan fitattun Yan wasan Faransa da suka hada da Kylian Mbappe da Karim Benzema da Antoine Griezmann inda tace kowacce kasa a Turai ta mayar da hankali akan su.
Wasu daga cikin Yan wasan da Faransa ta lashe kofin duniya ke tinkaho da su sun hada da N’Golo Kante da Sisoko da Fekir da Olivier Giroud da makamantan su.
Hankalin mutane zai karkata kan rawar da Karim Benzema zai taka bayan dawo da shi cikin tawagar Yan wasan Faransa sakamakon dakatarwar da aka masa tun daga shekarar 2015.
Kasar Portugal mai rike da kofin har yanzu tana kan ganiyar ta da zaratan 'yan wasa irinsu Cristiano Ronaldo wanda ake saran ya jagorancin kasar wajen kare kambin da suka ci a gasar da ta gabata.
Kasar Belgium wadda yanzu haka ke matsayi na farko a matakin FIFA cikin jerin kasashen da suka fi kowa tagomashi a duniya na da zaratan Yan awasa irin su Kevin de Bruyne da Romanu Lukaku da Eden Hazard da ake saran su cirewa kasar kitse a wuta.
Ita kuwa Ingila na dauke ne da tawagar Yan wasa matasa masu jini a jika wadanda ke neman suna a karkashin manajan su Gareth Southgate, yayin da Jamus ke kokarin farfadowa bayan rashin nasarorin da ta samu a shekarun baya.
Za’a kwashe makwanni ana fafatawa tsakanin kasashen dake wannan nahiyar, yayin da ake saran samun sabbin fitattun Yan wasan da za suyi suna domin samun kwangiloli masu tsoka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu