Isa ga babban shafi
Wasanni - Kwallon Kafa

Mai yiwuwa Eriksen ba zai sake buga kwallon kafa ba

Wani kwararren likita a fannin da ya shafi zuciya da hanyoyin numfashi Sanjay Sharma, ya ce mai yiwuwa dan wasan tsakiya na kasar Denmark Christian Eriksen ba zai sake buga kwallon kafa ba har abada.

'Yan wasan kasar Denmark cikin jimami da kaduwa bayan da Christien Eriksen ya yanke jiki ya fadi a yayin da suke tsaka da karawa da Finland a gasar cin kofin kasashen Turai ta Euro 2020. 12 /6/2021.
'Yan wasan kasar Denmark cikin jimami da kaduwa bayan da Christien Eriksen ya yanke jiki ya fadi a yayin da suke tsaka da karawa da Finland a gasar cin kofin kasashen Turai ta Euro 2020. 12 /6/2021. AP - Wolfgang Rattay
Talla

Ana tsaka da wasan da kasar sa Denmark ke karawa da Finland na gasar cin kofin kasashen Turai ta Euro 2020 a ranar Asabar da ta gabata, Eriksen ya yanke jiki ya fadi sakamakon tsayawar bugun zuciya da kuma daukewar numfashi.

Dan wasan dake taka leda a kungiyar Inter Milan ya tsallake rijiya da baya, sakamakon taimakon gaggawar da abokan wasansa suka bashi akan fili, kafin isowar jami’an lafiya a yayin da ‘yan kallo da sauran ‘yan wasa da jami’ai ke kallo cikin kaduwa, bayan farfadowarsa ne kuma aka garzaya da shi asibiti, inda har yanzu yake kwance cikin yanayi mai kyau kamar yada hukumar kwallon kafa ta Denmark ta sanar.

Sai dai Dakta Sharma, wanda Farfesa ne da ya kware a fannin likitancin kula da zuciya da hanyoyin numfashi wanda yayi aiki tare da Chrisrtien Eriksen a kungiyar Tottenham ya ce dan wasan na bukatar sa’a babba kafin samun damar komawa fagen kwallo kamar yadda ake bukata, la’akari da tsauraran dokokin kungiyoyi da hukumomin kwallon kafa, baya ga ma batun sake samun lafiyar sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.