Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Eriksen na fatan wakiltar Denmark a gasar cin kofin Duniya ta 2022

Dan wasan tsakiya na Denmark Christian Eriksen ya ce fatansa shi ne ganin ya wakilci kasarsa a gasar cin kofin Duniya da za ta gudana a Qatar cikin shekarar nan, duk da lalurar da ya ke da ita ta bugawar zuciya.

Christian Eriksen dan wasan tsakiyar Denmark.
Christian Eriksen dan wasan tsakiyar Denmark. MIGUEL MEDINA AFP/Archives
Talla

Eriksen mai shekaru 29 wanda kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan ta katse kwantiragin da ke tsakaninsu a disambar bara, saboda dashen da aka yi masa a zuciya biyo bayan faduwarsa a guda cikin wasannin gasar Euro da kasarsa ta doka cikin watan Yunin 2021, ya ce ba tun yanzu ba, fatansa shi ne wakiltar kasar tasa a Qatar.

Eriksen wanda tuni ya fara atisaye na radin kai a filin wasan tsohuwar kungiyar sa ta cikin gida yayin zantawarsa da kafar DR ya ce baya da tabbacin a iya zabensa zuwa gasar ta watan Nuwamba, amma dukkanin tunani da burinsa na kan gasar ta cin kofin duniya.

Dan wasan wanda ya bayyana shirin komawa Tottenham da taka leda a matsayin babbar nasara gareshi ya ce baya jin wani sauyi a jikinsa, kuma yana da cikakken karfin iya taka leda a kowanne irin wasa.

Acewar dan wasan yana bukatar a bashi damar taka leda a cikin tawagar kasa don nuna cewa yana da cikakkiyar damar iya wakiltar Denmark.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.