Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Dalilin da ya sa na kaurace wa Super Eagles - Mikel

Kyaftin din babban tawagar kwallon kafar Najeriya ta Super Eagles, John Mikel Obi ya bayyana dalilan da suka sa ya kaurace wa tawagara tun bayan gasar cin kofin Duniya da ta gudana a Rasha a shekarar 2018.

John Obi Mikel na Super Eagles.
John Obi Mikel na Super Eagles. NELSON ALMEIDA / AFP
Talla

Mikel dai bai fafata a ko daya daga cikin wasannin cancantar shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka ba, amma ya zo don a dama da shi a gasar, wadda za a fara a Masar ranar 21 ga watan Yunin nan.

Da yake jawabi ga wani taron manema labarai, tsohon dan wasan na Chelsea ya ce shawarar sa ba ta da nasaba da abin da ya faru a gasar kofin duniya ta 2018 din inda Najeriya ta rikito a matakin rukuni.

Ya ce bayan ya tattauna da kocin tawagar, Rohr ne, sai ya yanke shawarar janyewa daga tawagar, duba da cewa ya shafe shekaru 15 yana murza mata tamaula, farawa daga lokacin da ya fafata a gasar cin kofin duniya ta matasa ‘yan kasa da shekaru 17 da aka yi a Finland a shekarar 2003.

Obi ya ce baya ga haka, ya samu rauni a kafarsa wadda ya ke bukatar ya murmure sosai, don haka ya yi wannan hutu mai tsawo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.