Isa ga babban shafi
wasanni

Mikel Obi ya soke kwantiraginsa a China

Dan wasan Najeriya, John Mikel Obi ya soke kwantiraginsa da kungiyar kwallon kafa ta Tianjin Teda da ke buga gasar Lig ta China.

John Mikel Obi
John Mikel Obi REUTERS/Matthew Childs
Talla

Yanzu haka dan wasan na tsakiya zai raba gari da kungiyar duk da cewa, akwai sauran sama da kwantiragin shekara guda akan sa.

Mikel bai shiga cikin tawagar Tianjin ba wadda ta yi balaguro zuwa Spain don samaun horan bude fagen shiga sabuwar kaka.

A yayin zantawa da manema Labarai, dan wasan na Super Eagles ya ce, kawo yanzu bai tsayar da shawarar in da zai koma ba, amma akwai yiwuwar ya koma nahiyar Turai ko kuma ya ci gaba da zama a China a cewarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.