Isa ga babban shafi
wasanni

Mikel Obi ya fi muhimmanta Klob akan kasarsa

Kaften din tawagar Kwallon Kafa ta Super Eagles, John Mikel Obi ya yi biris game da mayar da hankali kan wasannin da Najeriya ke bugawa, in da a yanzu ya fi karkata hankalinsa kan kungiyarsa ta Middlesbrough da zummar jajircewar ganin nan gaba ya samu shiga gasar firimiyar Ingila.

John Mikel Obi
John Mikel Obi REUTERS/Matthew Childs
Talla

Dan wasan ya yi tanadin bayar da himmarsa 100 bisa 100 a Middlesbrough, in da a karshen mako zai shiga sahun tawagar farko da za ta kece raini da Norwich City a gasar rukuni na biyu na kasar Ingila.

Obi bai buga wasannin da Najeriya ta yi da kasashen Seychelles da Masar ba a baya-bayan nan, kuma raban da ya buga wa kasar tamaula, tun lokacin Gasar Cin Kofin Duniya ta bara a Rasha.

Sai dai har yanzu, kocin Super Eagles Gernot Rohr na kallon Obi a matsayin wani ginshike mai muhimmancin gaske a tawagar kasar musamman a daidai wannan lokaci da ake shirye-shiryen fara gudanar da Gasar Cin Kofin Kasashen Afrika a bana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.