Isa ga babban shafi
wasanni

Solskjaer ya zama kocin din-din-din a Man-U

Kungiyar Kwallon Kafa ta Manchester United ta tabbatar da Ole Gunnar Solskjaer a matsayin kocinta na din-din-din , in da ta kulla kwantiragin shekaru uku da shi.

Ole Gunnar Solskjaer
Ole Gunnar Solskjaer Svein Ove Ekornesvaag / NTB SCANPIX / AFP
Talla

Solskjaer mai shekaru 46 kuma dan asalin Norway, ya karbi aikin kocin rikon kwarya a Old Trafford a cikin watan Disamba domin maye gurbin Jose Mourinho bayan kungiyar ta yi fama da rashin karsashi.

Kocin ya sha kashi sau daya daga cikin wasanni 13 da ya jagoranci Manchester United a gasar firimiyar Ingila, kuma a halin yanzu tazarar maki biyu kacal ne tsakanita da Arsenal da ke matsayi na hudu a teburin gasar.

Sannan kuma ya kafa tarihin zama koci na farko da ya lashe wasanni shida na farko a jere a Manchester United, in da ya sha gaban Sir Matt Busby.

Solskjaer ya shafe kakanni 11 a matsayin dan wasa a Manchester United kuma shi ne ya jefa kwallon da ta bai wa kungiyar nasara a wasan karshe na gasar cin kofin zakarun Turai a shekarar 1999.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.