Isa ga babban shafi
Wasanni

UEFA ta kirkiro sabuwar gasar kwallon kafa a Turai

Hukumar kwallon kafa ta nahiyar turai UEFA ta tabbatar da kirkiro sabuwar gasa ta uku da za ta baiwa wasu karin kungiyoyi damar buga babbar gasa a matakin nahiyar.

Hukumar UEFA na ta kawo sauyi a gasannin kwallon kafa na nahiyar Turai.
Hukumar UEFA na ta kawo sauyi a gasannin kwallon kafa na nahiyar Turai. REUTERS/Regis Duvignau Livepic
Talla

Kwamitin zartarwar hukumar ta UEFA ne ya sanar da daukar matakin bayan taron baya bayan nan da yayi a Dublin, babban birnin Jamhuriyar Ireland.

Kari akan sabon sauyin shi ne, daga kakar wasa ta 2021/2022 da za’a soma sabuwar gasar da aka sanya wa suna UEL2, wato UEFA Europa League 2, hukumar za ta zaftare yawan kungiyoyin dake buga tsohuwar gasar Europa daga 48 zuwa 32.

Hakan zai baiwa manyan gasannin na turai da suka hada da Champions League, Europa League, da kuma sabuwar gasar ta Europa League 2, damar tsara fafatwa tsakanin kungiyoyi 32 kowannensu.

Wadanda za su rika halartar sabuwar gasar ta UEFA daga shekarar 2021 dai sun ne kungiyoyin kwallon kafa da suka kare a matsayi na 7 daga manyan gasannin kasashen turai, wadanda za’a gauraya su da wasu kungiyoyin da za su fito daga kananan gasannin dake gudana a nahiyar.

Idan aka soma sabuwar gasar ta UEFA Europa League 2, za’a rika buga ta ne kamar ta takwararta ta Europa a ranakun Alhamis, domin kaucewa shiga ranakun Talata da Laraba na wasannin gasar zakarun turai wato Champions League.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.