Isa ga babban shafi
Wasanni

Ban yi alkawarin lashe kofin nahiyar Afrika a 2019 ba - Rohr

Mai horar da tawagar kwallon kafar Najeriya ta Super Eagles Gernot Rohr, ya ce ba zai iya yin alkawarin lashe kofin gasar kwallon kafa ta kasashen Afrika ba, da Kamaru za ta karbi bakunci a shekarar 2019.

Mai horar da tawagar kwalon kafa ta Najeriya, Gernot Rohr.
Mai horar da tawagar kwalon kafa ta Najeriya, Gernot Rohr. Reuters/Peter Cziborra Livepic
Talla

A halin da ake ciki, Najeriya ce ke jagorantar, rukuni na biyar da take ciki, a wasannin neman cancantar halartar gasar cin kofin nahiyar Afrika da maki 9, yayinda Afrika ta Kudu ke mataki na biyu da maki 7. Kasashen Libya da Seychelles ke mataki na 3 da na 4 a rukunin.

A ranar 17 ga watan Nuwamba mai zuwa Najeriya zata yi tattaki zuwa birnin Johannesburg domin fafatawa da Afrika ta Kudu, wanda muddin ta lashe wasan, kai tsaye za ta samu tikitin halartar gasar cin kofin ta nahiyar Afrika.

A wasanni biyu da ta fafata na neman cancantar Najeriya ta lallasa Libya da kwallaye 4-0 a zagayen farko, zalika ta sake nasarar doke ta da kwallaye 3-2 a zagaye na biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.