Isa ga babban shafi
wasanni

PSG na fatan lallasa Real Madrid duk da rashin Neymar

Kungiyar kwallon kafa ta PSG da ke Faransa na ci gaba da fatan lallasa takwararta RealMadrid a gobe Talata, wasan da ta ke fatan kafa tarihi da shi duk kuwa da rashin tsadadden dan wasanta Neymar Dos Santos.

Ko a wancan karon ma dai, yayin haduwar Real Madrid da PSG, Real din ce ta lallasa PSG da ci 3 da 1.
Ko a wancan karon ma dai, yayin haduwar Real Madrid da PSG, Real din ce ta lallasa PSG da ci 3 da 1. CHARLY TRIBALLEAU / AFP
Talla

A cewar kochin kungiyar Unai Emery, sun dukkanin shirin da ya kamata don tunkarar wasan a gobe, yana mai cewa bai je paris kawai don ya karbi kudi ba, a a yaje ne don ya kafa tarihi ta yadda zai kai Club din matsayin da bai taba zuwa ba.

Emery ya ce yin kafada-da-kafada tsakaninsu da manyan Club irin su Real Madrid ne za su nunawa duniya irin karfin da kuma horon da ‘yan wasansu su ke da shi.

A watan daya gabata ne dai Neymar ya samu rauni a gwiwarsa matakin da babanshi ya ce yana bukatar makwanni shidda kafin murmurewa.

Ko a wancan karon ma dai, yayin haduwar Real Madrid da PSG, Real din ce ta lallasa PSG da ci 3 da 1.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.