Isa ga babban shafi
Wasanni

Ronaldo ya bukaci Madrid ta gaggauta sayen Neymar

Tsohon dan wasan gaba na Kungiyar Real Madrid dan kasar Brazil Ronaldo de Lima, ya shawarci tsohuwar kungiyar tasa ta Madrid da ta gaggauta saye tsohon dan wasan Barcelona da a yanzu ya ke PSG Neymar da Silva Santos.

Tsohon dan wasan Real Madrid kuma gwarzon dan kwallon kafa na duniya na Brazil, Ronaldo Luis Nazario de Lima.
Tsohon dan wasan Real Madrid kuma gwarzon dan kwallon kafa na duniya na Brazil, Ronaldo Luis Nazario de Lima. Reuters
Talla

A cewar Ronaldo, Madrid kungiya ce da ke bukatar kwararrun ‘yan wasa a koda yaushe, wanda kuma Neymar ke cikinsu.

A shekarar da ta gabata ne Neymar ya sauya sheka zuwa kungiyar PSG daga Barcelona kan euro miliyan 222, wanda ya sa shi zama dan wasa mafi tsada a duniya.

Sai dai duk da rahotannin da ke zagaya kafafen yada labarai kan cewa Neymar yana gaf da sauya sheka zuwa Madrid, Ronaldo de Lima ya musanta masaniyar tabbatuwar hakan.

A wani labarin kuma Ronaldo de Lima, ya ce Real Madrid zata iya sake lashe kofin gasar zakarun nahiyar turai karo na uku a jere, duk da tarin kalubalen da kungiyar ke fuskanta a kakar wasa ta bana, inda ta ke matsayi na 4 a teburin La liga, da kuma tazarar maki 19 tsakaninta da abokiyar hamayyarta Barcelona da ke matsayi na daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.