Sanchez na dab da sanin makomarsa -Arsene Wenger
Kocin kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Arsene Wenger ya ce nan gaba kadan dan wasa gaba na Kungiyar Alex Sanchez zai san makomarsa, amma ya rage ga dan wasan ya zabi inda hankalinsa zai fi kwanciya.
Wallafawa ranar:
Wenger na wannan bayanai ne bayan rashin nasarar da suka yi a hannun Bournemouth da ci biyu da daya a wasannin Primier wanda Sanchez bai halarta ba.
Sanchez dan kasar Chile mai shekaru 29 hankalinsa yafi karkata zuwa Manchester City amma kuma kawo yanzu Manchester United ta amsa bukatar Arsenal kan cinikin dan wasan.
Kungiyoyin biyu dukkaninsu sun nuna sha’awar sayen dan wasan a ranar karshe ta kasuwar cinikayyar ‘yan wasa a waccan kaka ta watan Agusta, amma kuma ba’a kai ga kammala ciniki ba har aka rufe kasuwar
Arsenal dai na bukatar yuro miliyan 39 don sayar da dan wasan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu