Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Arsenal ta yi watsi da tayin City akan Sanchez

Arsenal ta ki amincewa da tayin kudi fam miliyan 50 da da Manchester City ta yi wa Sanchez wanda ya dade yana tawayen ficewa daga kungiyar a bayan ya ki sabunta kwangilar shi.

Alexis Sanchez na son barin Arsenal
Alexis Sanchez na son barin Arsenal Reuters/Paul Childs
Talla

Arsenal na son City ta ba ta kudi hadi da Raheem Sterling. Manchester City kuma na son ta biya kudi ne ta mallaki dan wasan ba tare da ta ba da wani dan was anta ba.

Rahotanni kuma sun ce Chelsea na dab da karbar Chamberlin akan kudi fam miliyan 40.

Kodayake wasu rahotanni sun ce Chamberlin ya yi watsi da tayin saboda Chelsea ba za ta yi amfani da shi a tsakiya ba.

Dan wasan na fatan Liverpool za ta taya shi kafin rufe kasuwar cinikin ‘yan wasan.

Yanzu dai kalubalen da ke gaban Wenger shi ne cefanen ‘yan wasa kafin rufe kasuwa a ranar alhamis a yayin da ‘yan wasansa ke son ficewa Arsenal.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.