Isa ga babban shafi
Wasanni-Ingila

Akwai bukatar masoyan Arsenal su cigaba da goya mana baya - Wenger

Mai horar da Arsenal Arsene Wenger, ya bukaci magoya bayan kungiyar da su cigaba da mara musu bay aba tare da faduwar gaba ba.

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Arsene Wenger.
Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Arsene Wenger. Reuters/Stefan Wermuth
Talla

Kiran na Wenger, yazo ne bayan lallasa Arsenal da Liverpool ta yi da kwallaye 4 – 0, wasan da Wenger ya bayyana shi a matsayin iftila’I ga Klub din.

A lokacin wasan da aka fafata a jiya dai, an jiyo magoya bayan kungiya suna karajin ya kamata a kori Wenger.

To sai dai bisa dukkanin alamu a bangaren Wenger, kiraye-kirayen aikin banza ne wai an jefa agwagwa a ruwa, domin bayanda aka tambaye shi kan mai zai ce dangane da hakan, sai ya kada baki ya ce, aci gaba da hakuri da shi, idan har shi ne matsalar Arsenal, amma fa bai kamata masoya su juya musu baya ba, duk da shan kashin da suka yi, a karo na gaba rama abinda kungiyar ta Liverpool ta yi musu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.