Guardiola na ci-gaba da ba da tazara a Frimiya
Kocin Man city da ke jan ragamar teburin Frimiyar Ingila, Pep Guardiola, na ci gaba da bayyana farin cikinsa da koda David Silva wanda zura kwallayensa ya taimakawa kungiyar lalasa Swansea ci 4-0 da kuma nasara a manyan wasannin Frimiya 15.
Wallafawa ranar:
Silva ya zura kwallaye biyu, Kevin de Bruyne da Sergio Aguero kowa ya zura guda. City na da tazaran maki 11 tsakaninta da Man Utd da ke na biyu, yayin da Swansea ke karshen teburi.
Wannan shine wasa na 6 da ake doke Swansea a wasanni 9 da ta buga a gida a wannan kaka.
Yanzu dai City na da yawan kwallaye 52 a wasanni 17, inda Silva ke da 4 a wasanni 3, a karawarsu da West ham da kuma Man Utd.
Ita ma Leicester City ta samu nasaran ci 4-1 kan Southampton, a wasan da mai tsaron baya Harry Maguire ke cewa suna sake samun kwarin-guiwa da sabon kocinsu Claude Puel.
Puel dai tsohon kocin Southampton ne da ta kore shi a watan Yuni da ya gabata bayan rike kungiyar na kaka guda, da kai ta mataki da 8 a frimiya da wasan karshe na League cup.
A watan Oktoba Leicester ta dauko Puel, inda yanzu wannan shine wasa na 4 a jere da su ke yi cikin nasara.
A sauran wasannin kuma
Everton 1-0 Newcastle
Liverpool 0-0 West Brom
Man Utd 1-0 Bournemouth
Tottenham 2-0 Brighton
West Ham 1-0 Arsenal
A Bundesliga na Jamus
Hoffenheim 1-0 Stuttgart
Beyer Leverkusen 1-0 Werder Bremen
Bayern Munich 1-0 Koln
Schalke O4 3-2 Augsburg
Hertha Berlin 3-1 Hannover
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu