Isa ga babban shafi
Wasanni

Magoya bayan Bayern da PSG sun yi arangama gabanni fafatawarsu

An samu hatsaniya tsakanin Magoya bayan Bayern Munich da PSG a tashar jirgin kasa, gabanni haduwarsu yau talata a wasan zakarun Turai.

'Yan sanda sun tsaurara matakan tsaro bayan rikicin magoya bayan PSG da Bayern a tashar Munich
'Yan sanda sun tsaurara matakan tsaro bayan rikicin magoya bayan PSG da Bayern a tashar Munich Reuters
Talla

Rahotanni sun ce kusan magoya bayan kungiyoyin 60 ne su ka yi arangama da juna a tashar Munich, kafin ‘yan sanda su shiga tsakaninsu. Abin da ya kai ga fasa kan daya daga cikin magoya bayan PSG ta Faransa.

Yanzu haka ana tsare da magoya bayan PSG kusan 30 a Ofishin ‘yansanda, kazalika an cafke magoya bayan Bayern 3 da aka gani tattare da makami.

Magoya bayan PSG dubu 40 ake saran su kalli wasan na yau kai tsaye, don haka wannan hatsaniya ya haifar da furgaban barazanar tsaro.

Dukkanin Kungiyoyin biyu dai sun tsallake zuwa zagaye na kungiyoyi 16, sai dai Bayern na fatan lalasa PSG da akalla kwallaye 4-0, domin kammala matakin rukuni a matsayin zakara, bayan ruwan kwallaye 3-0 da PSG ta yi musu a watan Satumban da ya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.