Isa ga babban shafi
wasanni

Na ji dadin rashin haduwa da Najeriya a Rasha- Neymar

Dan wasan Brazil Neymar Da Silva ya bayyana farin cikinsa na rashin hada kasarsa da Najeriya a cikin rukuni guda a gasar cin kofin duniya da Rasha za ta karbi bakwanci a badi.

Dan wasan Brazil Neymar Da Silva Santos
Dan wasan Brazil Neymar Da Silva Santos REUTERS/Yves Herman
Talla

A lokacin da ya ke bayyana ra’ayinsa game da jadawalin da aka fitar a ranar Juma’a a birnin Moscow, Neymar wanda ke taka leda a PSG ta Faransa ya ce, wani sauki ne suka samu kan yadda suka yi sa’ar kaucewa haduwa da Najeriya da wasu kasashen Afrika a matakin rukuni.

A cewar Neymar, ‘yan wasan Afrika na nuna karfi sosai a yayin kokarin karbe kwallo daga abokan hamayya kuma sun cika gudu.

Brazil dai ta fada rukuni guda ne da Serbia da Costa Rica da Switzerland, yayin da da Najeriya ta fada rukunin Argentina da Croatia da Iceland.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.