Isa ga babban shafi
wasanni

Maradona zai bai wa Danjuma Kuti horo na musamman

Fitataccen dan kwallon kafar kasar Argentina da ya taba lashe kofin Duniya a shekarar 1986 da ya gudana a Mexico Diego Maradona ya nuna sha’awarshi kan matashin dan wasan gaba na Najeriya Danjuma Kuti.

Diego Maradona ya taba lashe kofin gasar duniya da ta gudana Mexico a shekarar 1986.
Diego Maradona ya taba lashe kofin gasar duniya da ta gudana Mexico a shekarar 1986. Reuters/Muhammad Hamed
Talla

Maradona wanda yanzu haka ke aikin horar da kungiyar kwallon kafa ta hadaddiyar daular Larabawa, ya yaba da hazakar matashin dan wasan mai shekaru 19 a duniya, lamarin da ya sa ya mayar da shi rukunin manyan ‘yan wasa don karbar horo na musamman.

Kuti wanda yanzu haka shi ne kan gaba wajen zura kwallaye a wasannin da kungiyar su ke fafatawa, ko a kakar da ta gabata shi ne ya kai kungiyar ga samun nasara bayan lallasa kungiyar kwallon kafa ta Al Wasl F.C a gasar matasa ‘yan kasa da shekaru 19.

Maradona wanda tuni ya mika bukatar sahalewa Danjuma Kuti taka leda a rukunin farko na kungiyar Fujairah wadda ‘yan wasa biyu ‘yan kasashen waje kadai ta ke sahalewa taka leda cikinta, inda kuma tuni wasu ‘yan wasa biyu da suka hadar da Omar Kossoko daga Faransa da kuma wani dan wasa daban uka nuna bukatar taka leda cikinta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.