Isa ga babban shafi
wasanni

Guardiola ya tsallake rijiya da baya

Hukumar kwallon kafar Ingila ba za ta dauki mataki kan kocin Manchster City Pep Guardiola ba game da yadda ya tinkari dan wasan Southampton, Nathan Redmond bayan wata fafatawa da kungiyoyin biyu suka yi a gasar Premier.

Kocin Manchester City, Pep Guardiola
Kocin Manchester City, Pep Guardiola Reuters/Andrew Yates
Talla

A ranar 29 ga watan Nuwamba ne Guardiola ya tinkari Redmond da maganganu bayan Raheem Sterling ya ci wa Manchester City kwallon da ta ba su nasara a wasan da aka yi a Etihad.

An dai zaci cewa, Guardiola na caccakar dan wasan ne na Southampton saboda yadda ya ke daga murya da kuma jefa hannayensa a yayin yi masa magana.

Sai dai Redmond ya ce, sam Guardiola bai fada ma sa maganar bacin rai, hasali ma yabon sa ya yi, in da bayyana shi a matsayin kwararren dan wasa a Ingila tare da tunatar da shi kan yadda ya kamata ya kai wa 'yan Manchester City hari.

A martanin da ya mayar ma sa, Redmond cewa ya yi yana buga wasa ne bisa umarnin kocinsa.

Amma dai  hukumar kwallon Ingila FA, ta bukaci Guardiola da ya kiyaye gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.