Isa ga babban shafi
Wasanni

Kaka ya zama dan wasan da ya fi karbar albashi

Tsohon dan wasan kungiyoyin Real Madrid, da AC Milan wanda a yanzu ke wasa a kungiyar Orlando City, Ricardo Kaka, ya zama dan wasan da yafi kowa karbar Albashi a gasar kwallon kafar kasar Amurka inda yake wasa a yanzu.

dan wasan gaba na tawagar kwallon kafar Brazil Ricardo Kaka.
dan wasan gaba na tawagar kwallon kafar Brazil Ricardo Kaka. REUTERS/Alessandro Garofalo
Talla

Kaka mai shekaru 35 zai rika karbar Fan miliyan 5.6 a matsayin albashinsa.

Wannan bayani yana kunshe ne cikin sanarwar da hukumar kwallon kafar Amurka ke fitar duk shekara kan ‘yan wasan da suka fi daukar albashi a kungiyoyin da ke gasar kasar.

Daga cikin wadanda ke biye da Kaka, akwai Sebestian Giovinco daga Italiya da ke wasa a kungiyar Toronto FC wanda zai karbi albashin fan miliyan 5.5, sai Micheal Bradely shi ma da ke kungiyar ta Toronto da zai ke amshe Fan miliyan 5.1.

Dan kasar Italiya da ke kungiyar NewYork City Andrea Pirlo ne hudu da Fan miliyan 4.6 sai David Villa tsohon na kungiyar Barcelona da shi me a yanzu ke kungiyar New York City da lbashin Fan miliyan 4.4.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.