Isa ga babban shafi
Wasanni

Buhari ya bada umarnin biyan Super Falcons

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bada umarnin gaggauta biyan ‘yan wasan Super Falcons kudadensu da su ke bin hukumar kwallonn kafar kasar.

'Yan wasan Super Falcons na Najeriya a lokacin zanga-zanga a birnin Abuja
'Yan wasan Super Falcons na Najeriya a lokacin zanga-zanga a birnin Abuja
Talla

Wannan na zuwa ne bayan zanga-zangar da kungiyar ta mata ta gudanar a majalisar tarayyar kasar don nuna bacin ransu da rashin biyansu kudin nasu bayan sun lashe gasar cin kofin Afrika ta mata a Kamaru.
 

‘Yan wasan sun yi zanga-zangar ce don janyo hankalin shugaba Buhari da ya halarci majalisar a jiya don gabatar da daftarin kasafin kudin shekara mai zuwa.

Tuni dai matan suka koma Otel din Agura bayan an yi musu alkawarin biyan su hakkokinsu.

Kowacce daga cikinsu na bukatar karbar  kimanin Dala dubu 23 da 650 kwatankwacin Naira miliyan 11 na Naira.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.