Isa ga babban shafi
Wasanni

Chelsea ta kara karfi a teburin Premier

Sakamakon nasarar da ta samu da ci daya mai ban haushi kan Sunderland, yanzu haka kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta bai wa Liverpool da Arsenal ratar maki shida a teburin gasar ta Premier ta Ingila, abin da ya kara mata karfin ci gaba da jan ragamar teburin.

Chelsea ta kara karfi a teburin gasar Premier ta Ingila
Chelsea ta kara karfi a teburin gasar Premier ta Ingila Reuters / Matthew Childs Livepic
Talla

Chelsea na da maki 40, yayin da Liverpool da Arsenal kowcce ke da maki 34.

Cesc Fabregas ne ya ci wa Chelsea kwallon daya tilo a minti na 40 da fara wasan na jiya, kuma sau 10 kenan a jere da kungiyar ta yi wasanni ba tare da an doke ta ba.

To sai a yayin da ‘yan wasan ke murnar kara karfi a saman teburin gasar, kocinsu Antonio Conte ya gargade su da su mayar da hankali kan fafatawar da za su nan da kwanaki uku da Crystal Palace.
 

A bangare guda,  Zlataran Ibrahimovic ya taimaka wa Manchester United samun nasara a fafatawar da ta yi da Crystal Palace a jiya Laraba, domin kuwa shi ne ya jefa kwallon karshe a ragar Crystal Palace ana saura minti biyu kacal a tashi wasan.

Paul Pogba ne ya fara zura kwallon farko a ragar Crystal Palace a minti na 45 kafin daga bisani ta farke ta hannun Mc Arthur a minti na 66.

A minti na 88 ne kuma, Pogba ya taimaka Ibrahimovc zura kwallon karshen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.