Isa ga babban shafi
Wasanni

FA ta ci tarar Chelsea da Manchester City

Hukumar kwallon kafar Ingila ta ci tarar Chelsea da Manchester City bayan ‘yan wasan kungiyoyin biyu sun tada hatsaniya a fafatawar da suka yi a Etihad a farkon wannan watan a gasar Premeir.

Hatsaniya ta kaaure tsanakin 'yan wasan Chelsea da na Manchester City a ranar 3 ga watan Disamba a Etihad
Hatsaniya ta kaaure tsanakin 'yan wasan Chelsea da na Manchester City a ranar 3 ga watan Disamba a Etihad
Talla

Hatsaniyar ta kaure ne a karshen wasan wanda Chelsea ta samu nasara da ci 3-1 a kan Manchester City, bayan an kori Sergio Aguero na City daga fili sakamakon harin da ya kai wa David Luiz.

Sannan kuma alkalin wasan ya sake korar Fernandinho na Man City saboda samun sa da laifin cukume Cesc Fabregas.

Yanzu haka dai Chesea za ta biya tarar Pam dubu 100 yayin da Manchester City za ta biya Pam dubu 35.

 

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.