Isa ga babban shafi
Najeriya

Super Falcons na zanga-zanga a Abuja

Tawagar kwallon kafar mata ta Najeriya Super Falcons na gudanar da zanga-zanga a kofar majalisar tarayyar kasar sakamakon rashin biyan su hakkokinsu bayan sun lashe gasar cin kofin Afrika ta mata a Kamaru.

Wasu daga cikin 'yan wasan Super Falcons da ke zanga-zanga kan hakokinsu a Abuja
Wasu daga cikin 'yan wasan Super Falcons da ke zanga-zanga kan hakokinsu a Abuja premiumtimesng.com
Talla

‘Yan wasan dai na bukatar janyo hankalin shugaban kasar ne Muhammadu Buhari wanda ke halartar Majalisar a yau Laraba don gabatar da kasafin kudin shekara mai zuwa.

Makwanni biyu kenan da ‘yan wasan suka lashe kofin a karo na takwas, amma har yanzu gwamnatin ba ta ba su kudinsu na alawus ba, abin da ya tilasta musu ci gaba da zama a Otel din Agura da ke birnin Abuja.

‘Yan wasan na bukatar hukumar kwallon kafar kasar ta biya kowanne daga cikinsu kimanin Dala dubu 23 da 650, kudaden da suka hada da bashin da suke bi a can baya da kuma na yanzu.

Sai dai hukumar ta NFF ta biya kowacce daga cikin ‘yan wasan Dala dubu 1 da 900 kwatankwacin Naira dubu 600, amma duk da haka sun ci gaba na nuna tirjiya.

A karo na farko kenan da kungiyar ta Super Falcosn ke zanga-zanga a Majalisar tarayyar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.