Isa ga babban shafi
wasa

Kroos ya tsawaita kwantiragi da Real Madrid

Dan wasan tsakiya na Jamus Toni Kroos ya amince ya tsawaita kwantiraginsa da Real Madrid har zuwa shekarar 2022 kamar yadda kungiyar ta sanar a ranar Laraba.

Dan  wasan Real Madrid Toni Kroos a Santiago Bernabeu
Dan wasan Real Madrid Toni Kroos a Santiago Bernabeu REUTERS/Andrea Comas
Talla

A shekarar 2014 ne dan wasan ya koma Real Madrid daga Bayern Munich a kan farashin Euro miliyan 25, yayin da ya buga mata wasanni 108, in da ya ci mata kwallaye hudu kacal.

Kroos dai na cikin tawagar da ta lashe wa Jamus gasar cin kofin duniya a shekarar 2014.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.