Isa ga babban shafi
Wasanni

Messi na shirin dawowa daga jinya

Gwarzon dan wasan Barcelona Lionel Messi na shirin dawo daga jinya, in da zai buga wa kungiyrsa wasan da za ta yi da Deportivo La Coruna a ranar Asabar mai zuwa a gasar La Liga. 

Lionel Messi na Argentina da ke taka leda a Barcelona
Lionel Messi na Argentina da ke taka leda a Barcelona Reuters
Talla

Wannan wasan dai, shi ne zai nuna ko Messi zai iya taka leda a karawar da Barcelona za ta yi da Manchester City a makon gobe a gasar cin kofin zakarun Turai.

Tun a ranar 21 ga watan Satumba ne, dan wasan ya tafi jinya bayan ya samu rauni a wasan da suka yi da Atletico Madrid, in da suka tashi kunen doki 1-1.

Dan wasan dai bai buga wasannin da Barcelona ta yi da Sporting Gijon ba, da kuma Borussia Moenchengladbach, har ma da wasan da suka lallasa Celta Vigo da ci 4-0.

Kana, bai buga wa kasarsa ta Argentina wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ba da ta yi da Peru da Paraguay.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.