Isa ga babban shafi
Wasanni

Rooney na cikin tsaka mai wuya

Kaften din tawagar kwallon kafar kasar Ingila, Wayne Rooney ya bayyana cewa, yana cikin tsaka mai wuya bayan an dauki matakin ajiye shi a banci a karawar da kasarsa za ta yi da Slovenia a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya a gobe Talata.

Dan wasan Ingila, Wayne Rooney
Dan wasan Ingila, Wayne Rooney Reuters/Gonzalo Fuentes
Talla

Kocin rikon kwaryar tawagar, Garerh Southgate ya bayyana cewa, matakin ajiye Rooney a banci na cikin tsari.

Rooney mai shekaru 30, bai samu nasarar zura kwallo a wasan da suka doke Malta da ci 2-0 a ranar Asabar ba, duk kuwa da cewa da shi aka fara wasan.

Sannan kuma ya sha ihu daga bagaren wasu magoya bayan Ingila a lokacin wannan wasa.

Kazalika, ita ma kungiyarsa ta Manchester United ba ta fara da shi a wasanni uku da ta buga a baya-bayan nan ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.