Isa ga babban shafi
Najeriya

Rashin kudi ya hana Super Eagles isa Zambia cikin lokaci

Matsalar kudi ta sa ‘Yan wasan Super Eagles na Najeriya ba za su isa Zambia ba cikin lokaci a karawar da za su yi na neman shiga gasar cin kofin duniya da za a gudanar a Rasha a 2018.

Sabon Kocin Super Eagles na Najeriya Rohr
Sabon Kocin Super Eagles na Najeriya Rohr NFF
Talla

Shugaban NFF Amaju Pinnick ya ce ba su iya daukar shatar jirgi da dawainiyar masaukin ‘yan wasan saboda matsalar karancin kudi kamar yadda ya shaidawa kwamitin wasanni na majalisar Dattijai.

An hada Najeriya ne dai a rukuni da ake ganin shi ne mafi zafi wanda ya kunshi Algeria da Kamaru da Zambia. A yau Alhamis ne ya kamata ace ‘yan wasan Super Eagles sun tashi zuwa Zambia domin fafatawa da Copper Bullets amma yanzu sai a ranar Asabar za su isa sannan su buga wasan a ranar Lahadi a filin wasa na birnin Ndola.

Super Eagles za su samu yin atisaye cikin lokaci kankani.

Pinnick ya ce wasu daga cikin ‘Yan wasan Najeriya da ke taka kwallo a Turai da kudinsu suka biya kudin jirgi zuwa Abuja sansanin da za su yi horo kafin zuwa Zambia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.