Isa ga babban shafi
Wasanni

Ramos na Real Madrid zai yi jinya

Dan wasan Real Madrid Sergio Ramos ya samu rauni a gwiwarsa a wasan da kasarsa ta Spain ta yi da Albania a gasar neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya a jiya Lahadi. 

Sergio Ramos na Real Madrid
Sergio Ramos na Real Madrid REUTERS/Kai Pfaffenbach
Talla

An dai sauya dan wasan mai shekaru 30 a minti na 80, ana dab da tashi wasan bayan ya fadi kasa.

A halin yanzu dai, ana kyatata zaton Ramos ba zai murza tamaula ba har na tsawon wata guda, abin da ke nufin cewa, ba zai samu damar buga wasannin La Liga guda hudu ba da suka hada da wasan da Real Madrid za ta yi da makociyarta Atletico Madrid.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.