Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Za a dinga yin canji sau hudu a gasar FA

Hukumar kwallon kafar Ingila na shirin bullo da wani sabon tsari na ba kungiyoyin kwallon kafa damar yin canjin ‘Yan wasa har sau hudu maimakon sau uku. Amma sai idan an kara lokacin wasan bayan kammala lokacin wasan na minti 90.

Marcus Rashford  na Manchester United ya canji Wayne Rooney a gasar cin kofin Turai a Faransa
Marcus Rashford na Manchester United ya canji Wayne Rooney a gasar cin kofin Turai a Faransa REUTERS
Talla

Tsarin zai kasance daga wasannin kwata fainal a gasar FA

Hukumar kwallon Ingila ta ce tana son aiwatar da tsarin amma sai hukumar wasannin kwallon kafa da ke tsara dokar kwallo wato IFAB ta duniya ta amince da sabon tsarin.

Kungiyoyin za su iya yin canji idan har sun kammala canjin yan wasa uku a lokacin wasan minti 90.

Sannan yanzu FA ta ce babu maimacin wasa a wasannin cin kofin FA idan har aka je zagayen kwata fainal.

An dai soma tsarin Karin canjin dan wasa na hudu ne a gasar Copa Amerika da Chile ta lashe a Amurka a bana.

A wasan karshe na lashe kofin FA da aka gudanar a watan Mayu tsakanin Manchester United da Crystal Palace sai da aka kara lokaci ana ci 1 da 1 kafin daga baya Man U ta jefa kwallo guda da ya ba ta nasara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.