Isa ga babban shafi
Wasanni

Vardy zai ci gaba da zama a Leicester City

Dan wasan Leicester City, Jamie Vardy ya jaddada cewa, zai ci gaba da zama a kungiyar, abinda ake ganin zai kara ma ta tagomashi.

Jamie Vardy ya taimaka wav Leicester City a nasarar da ta samu har ta lashe kofin Premier a karon farko tun bayan kafuwarta shekaru 132 da suka gabata.
Jamie Vardy ya taimaka wav Leicester City a nasarar da ta samu har ta lashe kofin Premier a karon farko tun bayan kafuwarta shekaru 132 da suka gabata. Reuters / Darren Staples
Talla

Leicester ce ta lashe kofin gasar Premier ta bana kuma Vardy ya taimaka ma ta wajen samun wannan nasarar, inda ya ci ma ta kwallaye 24.

Rawar da ya taka ne, tasa aka fara rade radin cewa da yiwuwar wata babbar kungiya ta yi zawarcin sa har ta dauke shi daga filin wasa na King Power.

Sai dai Vardy mai shekaru 29 ya nuna cewa, zai yi watsi da duk wani tayi da za a yi ma sa duk kuwa da irin makudaden kudaden da za a ba shi.

A shekara mai zuwa dai, Leicester City na cikin kungiyoyin da za su fafata a gasar cin kofin zakarun Turai.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.