Akwai sauran aiki a gaban Leicester City
Kungiyar kwallon kafa ta Leicester City na neman maki biyu kafin ta samu nasarar lashe kofin gasar Premier ta bana.
Wallafawa ranar:
Wannan kuwa na zuwa ne byan ta gaza samun maki uku a fafatawar da ta yi da Manchester United a Old Trafford a jiya Lahadi, inda suka tashi kunnen doki 1-1.
Akwai sauran aiki a gaban Leicester City wadda ke neman lashe gasar a karon farko tun bayan kafuwarta shekaru 132 da suka gabata.
To sai dai kungiyar za ta iya samun damar lashe gasar, idan dai Tottenham mai matsayi na biyu a teburin Premier ta gaza doke Chelsea a Stamford Bridge a fafatawar da za su yi a yau Litinin.
To idan dai Tottenham din ta samu nasara akan Chelsea, to hakan na nufin sai Leicester ta sake daura damara domin neman maki biyu a wasanni da za ta yi da Everton da Chelsea.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu