Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Ba zan damu da Guardiola ba- Mourinho

Jose Mourinho ya ce ba zai bari hankalin shi ya dauku ba akan adawar da ke tsakanin shi da Pep Guardiola, domin kada wata kungiya ta kutsu ta lashe kofin Firimiya da ya ke fatar lashewa Manchester United a karon farko tun 2013, lokacin da Sir alex Farguson ya bar kungiyar.

Josep Guardiola da José Mourinho a wasa tsakanin Real Madrid da Barcelona
Josep Guardiola da José Mourinho a wasa tsakanin Real Madrid da Barcelona Reuters
Talla

Guardiola da Mourinho sun san juna a La liga inda suka gwabza adawa a lokacin da Gurdiola ke horar da Barcelona, Mourinho kuma yana Real Madrid.

Yanzu manyan koca kocan na shirin farfado da adawarsu tsakanin Manchester United da Mourinho zai horar da kuma Manchester City da Guardiola zai soma aikin horar wa a kaka mai kamawa.

Guardiola da Mourinho zasu fara haduwa a wasannin share fagen kaka a Beijing a watan a ranar 25 na Yuli.

Mourinho ya ce ba zai damu da Guardiola ba idan dai har yana son lashe kofin Firimiya

Mourinho ya ce gasar Premier ta banbanta da sauran manyan gasanni a kasashen Turaim inda kungiya guda ke lashe kofi a jere da jere.

Mourinho wanda Chelsea ta sallama a watan Disemba a kakar wasan da aka kammala, yanzu ya sanya hannu kan kwantaragin shekaru uku da Manchester United.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.