Isa ga babban shafi
Premier League

FA ta caji Mourinho da rashin da’a

Hukumar kwallon kafa a Ingila ta caji kocin Chelsea Jose Mourinmho da laifin nuna rashin da a akan kalamansa ga alkalan wasa.

Kocin Chelsea, Jose Mourinho
Kocin Chelsea, Jose Mourinho Reuters/John Sibley
Talla

A ranar Assabar lokacin da Chelsea ta sha kashi a hannun West Ham Mourinho ya tunkari alkalin wasa Jonathan Moss da kalamai da aka danganta na rashin da’a.

FA kuma ta caji Chelsea da West Ham kan rashin daukar mataki akan hatsaniyar da ta biyo baya a fili a ranar Assabar da har ta kai aka ba dan wasan Chelsea Matic jan kati.

FA ta ba kungiyoyin biyu da Mourinho daga nan zuwa karfe 6 na yamma a ranar Alhamis domin su kare kansu.

Rahotanni d sun ce mai kungiyar Chelsea Roman Abramobich yana nazari akan makomar Mourinho, musamman idan rana ta baci a karawarsu da Liverpool a karshen mako.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.