Isa ga babban shafi
Premier League

Liverpool ta rike Arsenal

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya koka akan kwallon da alkalin wasa ya haramta Aaron Ramsey a ragar Liverpool, saboda Ramsy ya ci kwallon yana barawon gida.

Football - Arsenal v Liverpool - Barclays Premier League - Emirates Stadium - 24/8/15 Arsenal's Aaron Ramsey shoots at goal
Football - Arsenal v Liverpool - Barclays Premier League - Emirates Stadium - 24/8/15 Arsenal's Aaron Ramsey shoots at goal REUTERS
Talla

Arsene Wenger ya ce kwallo ce mai kyau Ramsey ya jefa a ragar Liverpool, kuma a cewarsa bai ga dalilin soke kwallon ba.

Liverpool dai ta rike Arsneal ne babu ci a Emirate, kuma wannan kalubale ne ga Arsenal inda yanzu wasanni biyu Wenger na bugawa ba kwallo a raga bayan ya sha kashi ci 2 da 0 a hannun West Ham United a ranar farko.

Balotelli zai koma AC Milan

Rahotanni daga Italiya sun ce AC Milan za ta karbi aron tsohon dan wasanta Mario Balotelli daga Liverpool na tsawon kakar wasa guda bayan kungiyoyin biyu sun cim ma yarjejeniya a jiya Litinin.

Jaridar wasanni ta Gazzetta dello ta fadi a shafinta na Intanet cewa a yau Talata ne AC Milan za ta diba lafiyar Balotelli, kuma idan an tantance zai fara wasan farko da kungiyar zata kara da Empoli a Seria A.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.