Barcelona ta lashe gasar Copa Del Rey
Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta lashe gasar Copa Del Rey a karo na 28 bayan ta doke Sevilla ci 2-0 a wasan karshe da suka fafata a jiya Lahadi.
Wallafawa ranar:
An shafe tsawon mintina 90 ba tare da jefa kwallo ko guda a raga ba, abinda ya sa aka kara wasu mintuna 30 na daban, kuma a wannan lokacin ne Jordi Alba na Barcelona ya fara jefa kwallo ta farko a ragar Sevilla kafin daga bisani Neymar ya sake zura wata.
Bayan fara wasan da minitina 36 ne, alkalin wasa ya sallami Javier Macherano na Barcelona saboda ya ja Kevin Gameiro na Sevilla har kasa.
Shi kuwa Luis Suarez ya fice daga filin wasan ne cikin kuka bayan ya samu rauni a yayin fafatawar.
Yanzu haka dai ana ganin mawuyaci ne dan wasan ya samu damar buga wa kasarsa ta Uruguy wasan da za ta yi da Amurka a gasar Copa America a watan gobe.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu