Isa ga babban shafi
Wasanni

Tsarin fadada Kulob zuwa 100 a Ingila

Akwai yiwuwar nan gaba a samu kungiyoyin wasa 100 da zasu fafata a gasa daban-daban ta wasannin kwallon kafa a Ingila, a wani gaggarumin sauyi da ake shirin aiwatar irinsa na farko tun bayan kirkiro wasanni premier League a shekarar 1992.

REUTERS/Rebecca Naden
Talla

Hukumar gasar League ta Ingila na son fito da wani sabon tsari wanda zai kunshi kungiyoyin wasa 20 a gasar wasanni daban-daban har guda biyar, daga kakar wasa ta 2019-20.

Wanda Hakan na nufin za a samu kungiyoyi 100 daga 92 da ake da su yanzu haka. Yanzu haka dai akwai kungiyoyi 24 a gasar Championship da League One da League Two.

A cewar Hukumar ta gasar League, sabon tsarin zai shawo kan matsalar da ake samu wajen tsara lokacin wasa, kana zai sa mambobin hukumar kara samun kudaden shiga.

Tuni dai wannan tsari ya samu amincewar Gasar Premier League da Hukumar FA

Sai dai ana bukatar amincewa kashin 90 cikin 100 na sauran kungiyoyi 72 na Championship da League One da League two, kafin a aiwatar da tsarin.

A taron karshen shekarar da za a gudanar a watan Yuli mai zuwa kungiyoyin za su bayyana goyon bayansu ko akasin haka. Koda dai an fara samun mabanbanta ra’ayi  kan wannnan tsari tsakanin kungiyoyin dake cewa ba a tuntubesu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.