Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya za ta dauko Bature kocin Eagles

Shugaban hukumar kwallon kafa a Najeriya Amaju Pinnick ya dage kan lalle sai bature zai dauko domin horar da ’yan wasan Super Eagles, wannan na zuwa ne bayan haramtawa kasar shiga gasar cin kofin nahiyar Afrika a badi.

Tambarin hukumar kwallon Najeriya
Tambarin hukumar kwallon Najeriya completesportsnigeria.com
Talla

Pinnick yace ba zai yi wasa da gasar cin kofin duniya ba da za a yi a Rasha a 2018, don haka ya zama wajibi a dauko kwararre daga waje.

Ya kare matakinsa, yana mai cewa sun gwada na gida amma ba wata riba.

An ba Sunday Oliseh dama, sannan aka dawo da Siasia wanda ya gaza doke Masar da ta haramtawa Najeriya zuwa Afcon.

Rahotanni dai na cewa tuni hukumar kwallon kafar ta Najeriya da dauki baturen Faransa da ba a bayyana sunansa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.