Isa ga babban shafi
Chan 2016

CHAN 2016: An fitar da Najeriya da Nijar a Rwanda

An yi waje da Najeriya da Nijar a gasar cin kofin Afrika ta matasa da ake gudanarwa a Rwanda bayan sun sha kashi a wasan karshe da aka fafata a rukuninsu na C.

Guinea ta doke Najeriya 1-0 a Rubavu, Tunisia  ta casa Nijar 5 da 0 a Kigali
Guinea ta doke Najeriya 1-0 a Rubavu, Tunisia ta casa Nijar 5 da 0 a Kigali CAF
Talla

Najeriya ta sha kashi ne hannun Guinea ci 1 da 0 wanda ya ba Guinea nasarar kai wa zagaye na gaba. Ibrahim Sankhon ne ya jefa Guinea kwallo a ragar Najeriya.

Tunisia kuma ta casa Nijar ne 5 da 0 wanda ya ba kasar nasara kai wa zagaye Kwata Fainal.

Tuni dai Kamaru ta tsallake zuwa zagayen kwata fainal a gasar bayan ta doke Jamhueriyyar Congo ci 3 da 1 a rukuninsu na B.

Yanzu kuma Kamaru za ta hadu ne da Cote d’Ivoire a kwata fainal.

Jamhuriyyar Congo kuma da ke bi mata a saman teburin rukuninsu zata kara ne da Rwanda mai masaukin baki

A ranar Asabar ne za a yi fafatawar a filin wasa na Amahoro a Kigali.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.