An kori Stephen Keshi daga matsayin kociyan Najeriya
Hukumar Kwallon Kafar Najeriya ta kori mai horas da ‘yan wasan kasar Stephen Keshi daga mukaminsa, inda hukumar ta sanar da nada Salisu Yusuf da kuma Shu’aibu Amodu a matsayin wadanda za su horas kungiyar kwallon kafar kasar Super Eagles har zuwa lokacin da za a nada kociya na dindindin.
Wallafawa ranar:
Sanarwar da hukumar ta NFF ta fitar bayan kammala wani taron koli ranar asabar a birnin Abuja, ta bayyana cewa an sallami Keshi ne sakamakon rashin taka rawar da ta dace a wasannin da kasar ta buga a baya-bayan nan.
Mataimakin shugaban hukumar ta NFF Barrister Seyi Akinwunmi, ya bukaci ‘yan Najeriya da kada su dauki wannan mataki a matsayin tozartarwa, inda ya ce an yi haka ne domin daukaka martabar kwallon kafa a Najeriya.
Wasu bayanai dai na cewa tube Stephen Keshi daga wannan matsayi ba ya rasa nasaba da shigarsa takarar neman mukamin mai horas da ‘yan wasan Cote D ‘Ivoire, bayan da mai horas da su Rene Herve ya ajiye makamin bayan kammala gasar neman kofin Afrika na 2015.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu