Isa ga babban shafi
Najeriya

Keshi zai ci gaba da horar da Super Eagles

Hukumar Kwallon Najeriya ta sake ba Stephne Keshi damar horar da ‘Yan wasan Super Eagles, bayan kwamitin kwararru ya amince a sabunta kwangilar shi. Keshi wanda ya kasa tsallakewa da Najeriya gasar cin kofin Afrika a Equatorial Guinea, Kwangilar shi ta kawo karshe tun lokacin da aka kammala gasar cin kofin duniya a Brazil.

Stephen Keshi, kocin Super Eagles na Najeriya
Stephen Keshi, kocin Super Eagles na Najeriya REUTERS/Henry Romero
Talla

Rahotanni sun ce Keshi ya samu goyon baya ne daga Shugaban kasa Goodluck Jonathan duk da suka da kalubale da ya ke fuskanta daga tsohon kocin Super Eagles Amadu Shu’aibu da sauran tsoffin ‘yan wasan Najeriya

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.