Isa ga babban shafi
Najeriya

Keshi da ‘Yan wasan Super Eagles sun kwashi kudi a Fadar Jonathan

‘Yan wasan Super Eagles na Najeriya sun isa gida a jiya talata kuma sun samu tarba ta musamman a Abuja babban birnin Tarayya wadanda suka kawo wa Najeriya kofin Afrika bayan kwashe tsawon shekaru 19.

'Yan wasan Super Eagles na Najeriya suna murnar lashe kofin Afrika birnin à Johannesburg kasar Afrika ta Kudu
'Yan wasan Super Eagles na Najeriya suna murnar lashe kofin Afrika birnin à Johannesburg kasar Afrika ta Kudu REUTERS/Siphiwe Sibeko
Talla

00:23

Ministan Abuja, Bala Muhammad

Ministan Abuja Bala Muhammed shi ne ya karbi tawagar ‘yan wasan a filin jirgin Nnamdi Azikwe.

Najeriya ta doke Burkina faso ne ci 1-0, kwallon da Sunday Mba ya zira mai dimbin tarihi a wasan karshe. Ahmed Musa yana cikin tawagar ta Super Eagle yace suna cike da murna kuma Add’ua ce ta kai su ga nasara.

Akwai buki na musamman da Gwamnatin Jonathan ta shiryawa ‘Yan wasan a Fadar shugaban kasa, kuma mai horar da su da makarabbansa da ‘Yan wasan sun kwashi kudi da wasu kyautuka daga Gwamnatin kasar.

00:28

Ahmed Musa Dan Wasan Super Eagles

Kocin Super Eagle Stephen Keshi ya samu kyautar kudi Naira Miliyan 10 daga Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan. Daniel Amokachi da sauran makaraban Keshi ko wannensu ya karbi kyautar kudi Naira .Miliyan biyar.

Haka kuma ‘Yan wasan Super Eagles kowannensu ya samu kyautar kudi Miliyan Biyar daga Gwamnatin Jonathan tare da raba ma su fiyale a Abuja babban birnin Tarayya.

Wannan bukin dai na zuwa ne bayan samun daidaituwa tsakanin Stephen Keshi da hukumar kwallon Najeriya, al’amarin da ya kai har Stephen keshi yace ya yi murabus kafin daga bisani ya janye matakin.

01:00

Kabiru Yusuf daga Fadar Jonathan a Abuja

Kuma kammala bikin ke da wuya, wasu ‘Yan Najeriya suka fara sukar Gwamnatin Jonathan wajen kin gudanar da aikace aikacen raya kasa, da kuma samar da ayyukan yi, amma aka karkatar da makudan kudade ga harkar wasanni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.