Isa ga babban shafi
Najeriya

Keshi ya yi murabus daga aikin horar da Super Eagles na Najeriya

Kocin Super Eagle Stephen Keshi ya ajiye aikin shi bayan taimakawa Super Eagles kawo karshen yunwar kofin Afrika tsawon shekaru 19. Keshi ya shaidawa wani gidan Rediyon Afrika ta kudu (SABC) cewa ya mika wa hukumar kwallon Najeriya takardar yin murabus dinsa bayan kammala wasan karshe amma a cewar shi har yanzu be samu amsa ba daga hukumar.

Kocin Super Eagles na Najeriya  Stephen Keshi yana rike da da kofin Afrika da suka lashe a kasar Afrika ta Kudu
Kocin Super Eagles na Najeriya Stephen Keshi yana rike da da kofin Afrika da suka lashe a kasar Afrika ta Kudu EUTERS/Siphiwe Sibeko
Talla

Mun lalabi Aminu Maigari shugaban Hukumar NFF amma ba mu kama shi ba, sai dai na kama Na hannun damar shi Patrick Pascal ya tabbatar da samun labarin murabus din Keshi amma yace shugabannin NFF ba su samu takarda ba a hukumance.

Rahotanni sun ce cewa akwai rashin jituwa tsakanin Keshi da shugabannin hukumar kwallon Najeriya, inda tun kafin Najeriya ta kara da Mali Keshi yace zai yi murabus saboda hukumar NFF ba ta yi na’am da aikin shi ba.

Keshi shi ne ya jagoranci tawagar Super Eagles da suka lashe kofin Afrika a 1994 wanda kuma a ranar lahadi ya jagoranci tawagar a matsayin koci da suka lashe wa Najeriya kofin Afrika karo na uku.

Keshi yace zai iya komawa aikin horar da ‘Yan wasan Mali.

Nasarar lashe kofin Afrika shi ne ya mamaye daukacin Jaridun Najeriya, inda jaridar Guardian a kudancin kasar ta buga babban labaranta mai taken “Najeriya ce, Super Eagles sun lashe kofin Afrika, Shugaba Jonathan da sauran shugabanni sun jinjina ma su".

Jaridar Punch ta buga babban labarinta ne mai taken “Sarakunan Afrika, Super Eagles sun kawo karshen yunwar kofin Afrika tsawon shekaru 19”.

Super Eagles na Najeriya sun kwashi kudi Dala Miliyan 1.5, kuma Najeriya ce zata wakilci Afrika a gasar cin kufin Zakarun Nahiyoyin Duniya da za’a gudanar a Brazil a watan Juni.

Shugaban hukumar CAF ta mika sakon murna ga Afrika ta Kudu ga kokarin daukar nauyin gasar Afrika karo na 29 ba tare da wata tangarda ba.

A bana ne a kasar Afrika ta kudu Hukumar CAF tace ta fi samun cinikin tikitin shiga kallon wasannin fiye da sauran kasashen da aka gudanar da gasar a baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.