Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya ta lashe kofin Gasar Nahiyar Afrika

Najeriya ta kawo karshen farin rashin lashe Gasar Cin Kofin Nahiyar Afrika da aka gudanar a kasar Afrika ta Kudu, bayan ta kwashe shekaru 19 bata samu damar lashe gasar ba. Nasarar da Najeriya ta samu ta biyo bayan doke Burkina Faso da ci 1-0 inda dan wasan Najeriya, Sunday Mba ya zira a kwallo a minti na 40 kamin aje hutun rabin lokaci. Rabon dai da najeriya la lashe wannan gasa tun a shekarar 1994 kuma wannan shine karo na uku.  

'Yan wasan Najeriya a lokacin da suka lashe Gasar Cin Kofin Nahiyar Afrika
'Yan wasan Najeriya a lokacin da suka lashe Gasar Cin Kofin Nahiyar Afrika
Talla

Najeriya dai ta fara lashe kofin ne a shekarar 1980 bayan ta doke Algeria da ci 3-0 a Jihar Lagos, sannan a bayan shekaru 14 ta sake lashe gasar bayan doke Zambia da 2-1 a Tunisia.

Sau uku kacal kuma Najeriya da Burkina Faso suka hadu a tarihin gasar ta Nations Cup, da farko tun ana kiran kasar Burkina Faso da Upper Volta, wato a shekarar 1978 Najeriya ta doke ta da ci 4-2, sannan sai kuma haduwar da suka yi a farkon wannan gasar inda suka tashi da ci 1-1.

Sai kuma wannan haduwar ta karshe, inda Najeriya ta samu galaba akan Burkina Faso.

Wannan nasara dai ta haifar da abubuwa da dama, inda a Kocin na Super Eagles, Stephen Keshi ya zama mutum na biyu a Nahiyar Afrika da ya taba lashe gasar a matsayin dan wasan da kuma mai horar da ‘yan wasan, bayan Mahmud El Gohary na kasar Masar.

Najeriya kuma zata samu kyautar kudi Dalar Amurka miliyan 1.5 kana zata wakilici Nahiyar ta Afrika a gasar zakarun nahiyoyin duniya, inda zata kara da kasashe da suka hada Spain da Tahiti da Uruguay a rukuninta.

Har ila yau, dan wasan Najeriya, Emmanuel Aminike tare da Dan wasan Ghana Mubarak Wakaso ne suka lashe kyautar ‘yan wasan da suka fi zira kwallaye a gasar da kwallaye hudu-hudu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.