Isa ga babban shafi
Wasanni

Barcelona ta doke Athletico Bilbao ci 6-0 a La Liga

Kocin Barcelona Luis Enrique ya kare matakin daya dauka Jiya Lahadi na cire Lionel Messi bayan hutun rabin Lokaci a wasansu na La liga da kungiyar ta doke Athletic Bilbao da ci 6-0.

Luis Suarez na Barcelona
Luis Suarez na Barcelona REUTERS/Sergio Perez
Talla

A cewar Luis ya cire Messi ne domin kare lafiyar dan wasan da aka ce yana fama da dan rauni, duk da dai ana gani cewa rauni bai ci a fida shi daga wasan ba.

Wasan na jiya dai yazo wa Barcelona da sa’a duk da dai an buga wasan ne tsakanin ‘yan wasa 11 da 10 na Athletico, saboda jan katin da aka baiwa mai tsaron gida Athletico Gorka Iraizoz bayan kayar da dan wasa, kuma Messi ne ya ci ta kwallon farko a bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Suarez ne ya zurawa Barcelona kwallaye 3 cikin 6 da kungiyar ta ci, yayin da Neymar ya zura guda, sai Rakitic da shima ya zura kwallo guda.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.