Isa ga babban shafi
Najeriya

Sunday Oliseh zai gaji Keshi a matsayin kocin Super Eagles

Hukumar kwallon kafar Najeriya NFF ta ce sun samu fahimtar juna da tsohon kaftin na Super Eagles Sunday Oliseh akan yarjejeniyar zama kocin babbar kungiyar kasar Super Eagles wanda zai gaji Stephen Keshi da ta sallama.

Sunday Oliseh zai gaji Stephen Keshi a matsayin kocin Super Eagles
Sunday Oliseh zai gaji Stephen Keshi a matsayin kocin Super Eagles FIFA
Talla

Hukumar NFF tace ta samu jituwa tsakaninta da Sunday Oliseh, bayan shugaban hukumar Amaju Pinnick ya gana da shi a London.

Amma hukumar tace ba ta ida kammala yarjejeniya da tsohon dan wasan na Najeriya ba.

A makon jiya ne Hukumar NFF ta kori Stephen Keshi, tana mai alakanta rashin jajircewa da mayar da hankali ga aikinsa, musamman bayan wasu rahotanni sun ce kocin na Najeriya ya nemi aikin horar da ‘Yan wasan kasar Cote d’Ivoire duk da yana da yarjejeniya da Najeriya.

Oliseh dai yana cikin tawagar Najeriya da suka lashewa kasar kofin Afrika a Tunisia a shekarar 1994, kuma yana cikin tawagar kasar da suka bugawa Najeriya gasar cin kofin duniya a 1994 da 1998 inda Super Eagles ta tsallaka zuwa zagaye na biyu.

Oliseh kuma yana cikin ‘Yan wasan Najeriya da suka lashe zinari a wasannin Olympics a shekarar 1996.

Oliseh ya taka kwallo a Turai a manyan kungiyoyi da suka hada da Ajax da Juventus da Borussia Dortmund.

Oliseh ya samu shedar zama koci daga hukumar FIFA, wanda ya horar da wata karamar kungiyar Belguim tsakanin 2008 zuwa 2009.

Sai dai kuma wasu sun soki matakin hukumar NFF na daukar Oliseh, wadanda ke ganin ba ya da wata kwarewa ta horar da 'Yan wasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.